Abubuwan da ya Kamata Mutum ya Sani Game da Zakkatul Fitr(Zakkar Fidda Kai) – Sheikh Aminu Daurawa

 

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jahar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas’alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malamin ya yi bayanin cikin sauki abubuwan da ya kamata mutum ya sani game da Zakkatul Fitr (Zakkar fidda kai).

ZAKKAR FIDDA KAI

Wannan wata sadaka ce da ake kira zakkar fidda kai, sadaka ce da ake yi idan an ƙare azumin watan Ramdhan, kafin a yi sallah Idi.

Malamai sun faɗi hikimomin da ke cikin wannan sadaka.

Na farko: Tana tsarkake mai azumi daga zunuban da ya aikata da bakinsa yayin azumi.

Na biyu: Yaƙi ne da yunwa da kuma kyautatawa talakawa, kamar yadda hadisi ya zo daga Manzon Allah ﷺ, ana samun lada mai yawa a wannan sadaka, kamar yadda Manzon Allah ﷺ ya ke cewa; “Wanda ya bayar da wannan sadaka kafin a tafi sallar idi, Allah ﷻ zai karba masa. Wanda kuma ya bayar bayan an dawo daga sallar idi ta zama sadaka ce kamar sauran sadakoki.” Ibn Maja ne ya raiwato shi.

Sannan sadaka ce da ke nuna godiyarka ga Allah ﷻ da ya raya ka har Shekara ta zagayo kana lafiya.

ZAKKAR FIDDA KAI TANA DA SHARAƊI HUƊU

Na farko: Mai bayarwa ya zamo

Na biyu: Ya kasance mawadaci.

Na uku: Ya zamo an ba da ita a kan lokaci.

Na huɗu: A bada ita ga wanda ya cancanta.

WAƊANDA ZAKKAR FIDDA KAI TA ZAMA WAJIBI A KANSU

Wannan zakka tana zama wajiba a kan kowani Musulmi babba da yaro, mace da namiji, tsoho da tsohuwa, ɗa da bawa.

MATAKAN DA AKE BI WAJEN FITAR DA ZAKKAR FIDDA KAI GUDA UKU NE

Ya halatta a bayar da ita kafin zuwan ranar Idi da kwana ɗaya ko biyu.

Lokacin fitar da zakkar fidda kai yana farawa ne daga faɗuwar ranar ashirin da tara (29 ga watan Ramadan zuwa kafin a tafi sallar Idi.

An so a fitar da wannan zakka ranar SAllah kafin a tafi Idi. Ba ya halatta a jinkirta ta har sai an dawo Idi.

Zakkar fidda kai ana bayar da ita ne gwargwadon kwano ɗaya, wato mudannabi huɗu kenan.

NAU’IN ABINCIN DA AKE BAYARWA

A zakkar fidda kai ana bayar da kowani nau’in abincin da mutanen garin suke amfani da shi, kamar dangin su alkama, shinkafa, gero, dawa, masara, da wake.

Amma an fi so a bayar da abin da mutum zai iya sarrafawa ya ci cikin sauƙi, kamar shinkafa, alkama ko filawa.

WAƊANDA AKE BA ZAKKAR FIDDA KAI SU NE TALAKAWA DA MISKINAI

Wasu malaman suna ganin ya halatta a zakkar fidda kai mutum ya bayar da kuɗi maimakon abinci, amma idan wanda za a ba ya fi buƙatar kuɗin, wataƙil wani ya ba shi abincin amma ba kuɗin dafawa.

Wajibi ne idan ka fitar wa kanka zakkar fidda kai, sai kuma ka fitar wa da ‘ya‘yanka da matarka da waɗanda ke ƙarƙashinka idan ba su da hali.

Zakkar fidda kai ana bayar da ita ne a garin da ake zaune sai dai idan duka garin masu arziƙi ne shi ne za a iya fitar da ita wani garin daban.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here