Darikar Tijjaniya ta Tabbatar da Nadin Sanusi Lamido Sunusi II a Matsayin Khalifa na Darikar ta Tijjaniya

 

Darikar Tijjaniya ta tabbatar da nadin Sanusi II a matsayin Khalifa na darikar ta Tijjaniya.

A baya cikin watan Maris, an sanar da Sanusi a matsayin Khalifa na darikar Tijjaniya a Najeriya.

An ruwaito cewa, Sheikh Mahi Ibrahim Inyass ne ya tabbatar da nadin nasa a kasar Senegal.

Sheikh Mahi Ibrahim Inyass, babban Khalifa na darikar Tijjaniya, ya nada Sanusi Lamido Sanusi II a matsayin Khalifa na darikar Tijjaniya a Najeriya a ranar Lahadi a Senegal.

A watan Maris, an sanar da tsohon sarkin a matsayin Khalifan darikar Tijaniyya a taron shekara-shekara da ake yi a Sakkwato, TheCable ta ruwaito.

Bangarori biyu na darikar sun nada tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) a matsayin Khalifansu a lokacin bikin Mauludin Inyass.

Auwal Shuaib, sakatare-janar na darikar Tijjaniya ta Najeriya, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.

“Babban Khalifa na Tijjaniyya Sheikh Mahi Ibrahim Inyass, a hukumance yana bayar da sanarwar nada tsohon Sarkin Kano, Alh Muhammad Sanusi II, a matsayin Babban Khalifa a Najeriya,” in ji sanarwar.

“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya datar da shi zuwa ga sauke nauyin da ke kansa kuma ya sanya hakan ya zama mai amfani ga dan adam, Amin.”

Wannan ci gaban na zuwa ne shekara guda bayan da Abdullahi Ganduje, gwamnan Kano, ya cire Sanusi daga kujerar sarautar Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here