E-Naira: Babban Bankin Najeriya ya Kaddamar da Shafin Kudin Yanar Gizo
Babban bankin Najeriya ya kaddamar da shafin kudin kasar na yanar gizo mai suna E-Naira.
Kamar yadda daraktan yada labarai na CBN, Osita Nwanisobi ya sanar, an bude shi a yau Litinin.
Sai dai kuma, duk da bude shi da aka yi, ba za a fara cinikayya ba sai an kaddamar a ranar 1 ga Oktoba.
FCT, Abuja – Babban bankin Najeriya, CBN, ya kaddamar da shafin yanar gizo na e-naira kafin a kaddamar da shi a hukumance ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.
Read Also:
Daily Trust ta rawaito cewa, shafin ya fara aiki amma har yanzu ba a fara harkar cinikayya da shi ba.
Babban bankin Najeriya ya saki shafin mai adireshi www e-naira.com a ranar Litinin.
Daraktan yada labarai na babban bankin, Osita Nwanisobi, ya tabbatar da wannan cigaban ga manema labarai.
Ya tabbatar da cewa, duk da shafin ya fara aiki, babu wata harkar cinikayya da aka aminta da farawa a kai har sai ranar 1 ga watan Oktoban 2021.
Tunin shafin ya samu maziyarta sama da miliyan daya a halin yanzu.
Dubawar da Daily Trust ta yi wa shafin ya nuna cewa, bayanan ayyuka ne kadai a shafin.
Amma kuma an bukaci masu ziyartar shafin da su sauke manhajar a wayoyinsu.