Shugaban Turkiyya, Erdogan ya yi Barazanar Korar Jakadun Kasashe 10
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce zai janye matsayin diflomasiyya na jakadun kasashen waje guda 10 wadanda suka nemi a saki guda 10 wadanda suka nemi a saki wani mai fafutika, Osman Kavala.
Read Also:
Mista Erdogan ya ce jakadun 10 sun kunshina kasashen NATO Amurka da Faransa – matakin zai kasance na farko na korar jami’in diflomasiyya.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta gayyaci jakadun guda 10, saboda abin da ta bayyana a matsayin “kalaman nuna rashin da’a” na kiran a gaggauta warware matsalar Osman Kavala.
Ya kasance a gidan yari tun shekarar 2017, ana tuhumarsa da laifin tallafa wa zanga -zanga da kuma shiga cikin juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekarar 2016, zarge-zargen da ya musanta.