Bashin da Ake Bin Najeriya ya Tashi Zuwa N46.25trn – DMO
Ofishin Kula da Basussuka a Najeriya ya bayyana cewa bashin da ake bin ƙasar ya tashi zuwa N46.25trn ya zuwa watan Dismanban 2022.
A wata sanarwa da Ofishin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an samu ƙarin tiriliyan bakwai cikin basukan da ake bin ƙasar.
Read Also:
DMO ya ce dalilin da ya sa aka samu ƙarin bashin shi ne saboda ciyo sabbin basuka da gwamnatin tarayya da ta jihohi suka yi domin gudanar da manyan ayyuka da kuma cike gibin kasafin kuɗi.
Ofishin ya ce kokarin da gwamnati ke yi na ƙara samun kuɗaɗen shiga daga ɓangaren albarkatun mai da kuma ɓangarorin da ba na mai ba, za su taimaka a gudanar da ayyuka ba tare da cin bashi ba.
Al’ummar Najeriya dai na ci gaba da nuna damuwa kan irin bashin da ƙasar ke ciwowa.
A shekarar 2005 ne ƙasar ta cimma wata yarjejeniyar yafiyar bashi da ƙungiyar Paris Club, abin da ya sanya aka yafe wa ƙasar dala biliyan 18 daga cikin bashin da ake bin ta.