Oyo: An Samu Wasu Bata Gari Sun Wawashe Gidan Sanata a Najeriya

Wasu fusatattun matasa sun afka gidan sanata mai wakiltar Mazaɓar Oyo ta Tsakiya, Teslim Folarin, inda suka wawashe kayayyaki.

Jaridar Premium Times ta ruwaito a yau Asabar cewa matasan sun yi awon gaba da babura da firji da injinan niƙa da sauran kayayyaki na tallafa wa mutane a gidansa na Ƙaramar Hukumar Oluyole ta Jihar Oyo.

Kazalika, jaridar ta ruwaito yadda aka wawashe gidan tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai Yusuff Lasun a Jihar Osun.

Haka nan wasu matasa sun yi yunƙurin shiga ginin Arts and Culture da ke Area 10 a Abuja domin ɗebe kayan abinci na tallafin annobar korona da suka ce an ajiye a ciki

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here