Bude Makarantu: Gwamnatin Jahar Bauchi ta Saka Ranar 18 ga Watan Janairu
Gwamnatin jahar Bauchi ta sanar da ranar da zata bude dukkan makarantun ta.
Gwamnatin jahar ta bayyana kulawa da kiyayewa da ta shirya yi don kaucewa kamuwa da COVID-19.
Gwamnatin ta kuma shaida adadin adabin makarantun ta 4,816 ne duka za su bude a ranar.
Read Also:
Duk da shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yanke na sake duba yiwuwar bude makarantu a ranar. 18 ga watan Janairu gwamnatin jahar Bauchi ta ce dukkan makarantu 4,816 da ke jahar za su koma karatu a zangon farko na 2020/2021 na Litinin 18 ga Janairu, TVC News ta ruwaito.
Kwamishinan Ilimi na jahar Bauchi, Aliyu Tilde ya fada a ranar Laraba cewa makarantun za su bi ka’idojin COVID-19 na kiyaye cinkoso, sanya takunkumin fuska, wanke hannu da “duk wani matakin da zai hana yaduwar cutar.”
Kwamishinan ya jaddada cewa za a fara cikakken aikin ilimi a dukkanin makarantun firamare da kananan sakandare 4,600, da kuma manyan makarantun sakandare 216, a fadin kananan hukumomin 20 na jahar a ranar da aka kayyade.
Ya kuma ba da tabbacin cewa Gwamnati ta yi abin da ake bukata ta hanyar tsaftace dukkan “makarantu, gami da manyan makarantun nan hudu da ke akwai, don kiyaye duk wani abin da zai faru.”