Gwamnan Bauchi ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jahar
Gwamnan jahar Bauchi, Bala Mohammed ya nada Dr Aminu Gamawa a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gidan gwamnati.
Nadin Dr Gamawa na zuwa ne bayan gwamnan ya sallami tsohon shugaban ma’aikatan Dr Ladan Salihu da wasu masu rike da mukamman siyasa a makon da ta gabata.
Kafin nadinsa a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Dr Gamawa ya rike mukamin kwashinan kasafin kudi da tsarin tattalin arziki na jahar Bauchi.
Gwamna Bala Mohammed na jahar Bauchi ya nada Dr Aminu Hassan Gamawa a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jahar Bauchi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
The Punch ta ruwaito cewa Muktar Gidado, mai magana da yawun gwamnan ne ya sanar da nadin da ya ce zai fara aiki nan take.
Read Also:
Gamawa ne tsohon kwamishina na kasafin kudi da tsarin tattalin arziki na jahar Bauchi.
A ranar Laraba da ta gabata ne Gwamna Mohammed ya sauke masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa da suka hada da sakataren gwamnati, Sabiu Baba, Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Dr Ladan Salihu, kwamishinoni da mashawarta 21. Ladan Salihu shine tsohon Dirketa Janar na Rediyo Nigeria wato FRCN.
Gamawa ya fito ne daga karamar hukumar Gamawa da ke jahar Bauchi, lauya ne, malami, kwararre wurin tsare-tsaren gwamnati kuma ma’aikacin gwamnati ne.
Sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnan ya yi aiki a hukumomi da maaikatu da dama, makarantu da kungiyoyi taimakawa al’umma. A cewar sanarwar da Gidado ya fitar, Gamawa ya yi digiri na biyu da digir-gir daga Jami’ar Harvard da ke kasar Amurka.
‘Yan bindiga sun afka wasu unguwanni a Zaria sun sace mutane da dama.