A Rashin Sani Gwamna Ganduje ya Taka Hoton Kwankwaso – Malam Muhammad Garba
Gwamnatin jahar Kano ta bayyana cewa bada sanin gwamna Ganduje ya taka hoton kwankwaso ba.
Kwamishinan labarai na jahar, Malam Muhammad Garba, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Kano.
Yace kowa yasan gwamna Gandune da ƙaunar zaman lafiya da girmama mutane, ba zai taba yin haka da gan-gan ba.
Gwamnatin jahar Kano ta bayyana cewa taka hoton kwankwaso da gwamna Ganduje yayi ba dagangan bane kuma ba shiryayyen abu bane, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Kwamishinan labarai na jahar, Malam Muhammad Garba, shine ya faɗi haka, yace hoton da ake yaɗawa na gwamna Ganduje yana taka Fastar kwankwaso a wajen taron APC da ya gudana ranar Asabar, ba da sanin mai girma gwamna bane.
Read Also:
Kwamishinan ya ƙara da cewa kowane irin banbancin siyasa ke tsakanin mutanen biyu, ba halayyar gwamna Ganduje bane yayi irin wannan abun ga wani ɗan siyasa.
Yace yayin da ake cigaba da yaɗa hotunan, har wasu sun fara sukar gwamna akan lamarin saboda wata manufar su ta siyasa, lamarin zai iya zama wata babbar matsala idan ba’a fito an bayyana gaskiya ba.
Da yake bayyana ainihin abinda ya faru, kwamishinan yace:
“A lokacin taron, dandazon mabiya ɗariƙar kwankwasiyya suka sauya sheƙa zuwa APC, lokacin da aka kira gwamna yazo yayi jawabi sai waɗannan tsoffin yan kwankwasiyya suka yi layi a hanyar gwamnan domin nuna goyon bayan su ga gwamnan.”
“Wasu daga cikinsu suka fara watsi da hotunan tsohon gwamnan, ɗaya daga cikin hotunan ya faɗo kan kafet din da gwamna zai taka ya wuce, ba tare da sanin Ganduje ba ya taka ya wuce.”
Malam Garba yace kowa yasan gwamna Ganduje da son zaman lafiya da girmama mutane, bai kamata ace ana sukar sa kan abinda yayi bad saninsa ba.