Gwamnonin Jam’iyyar PDP Sun Fitar da Tsarin Tumbuke Jam’iyyar APC a Zaben 2023

 

Gwamnonin Najeriya karkashin jam’iyyar PDP sun yi taro don karbe mulkin APC a zaben 2023.

Gwamnonin sun bayyana cewa, suna son fitar da wani tsari ne wanda zai basu damar karbar mulkin.

Hakazalika sun bukaci addu’ar nasara daga bakin ‘yan Najeriya domin kuwa Allah yana tare dasu.

Gwamnonin da ke karkashin jam’iyyar PDP sun hadu a oyo, babban birnin jahar Akwa Ibom don yin shawarwari kan yadda za a tumbuke jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023, Premium Times ta ruwaito.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, gwamnonin suka yi alkawarin samar da tsarin da jam’iyyar ke bukata don dawowa kan mulki a matakin tarayya a 2023 Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya yi wannan alkawarin a wata liyafa da gwamnatin jahar Akwa-lbom ta shirya, gabanin taron kungiyar a Uyo.

Tambuwal ya ce gwamnonin PDP ba za su ba ’yan Najeriya kunya ba a aiwatar da burinsu na ganin jam’iyyar ta dawo kan mulki a 2023.

ya ce “Wadannan taurarin shugabannin gwamnonin PDP a jahohinsu da gogewarsu ta siyasa sun kafu ne da yardar Allah ta hanyar addu’o’inku, goyon baya da hadin kai, don ceto Najeriya.

“Aiki ne wanda dole ne mu yi shi domin girman Allah da daukakarsa shi kadai.

“Allah yana tare damu, mun yanke shawara a matsayinmu na shugabanni, don samar da wannan tsarin na samun nasarar shugabancin PDP a wannan kasar, a shekarar 2023.”

Tambuwal ya bukaci ‘yan Najeriya su saka kasa a addu’a don magance matsalar tsaro Jaridar Today ta lura cewa gwamnan ya bukaci dukkan ‘yan kasa, musamman shugabannin addinai, da su ci gaba da yi wa kasar nan addu’a, musamman kan yanayin tsaro a kasar.

“Muna bukatar addu’a. Allah yana tare da jama’arsa ko yaushe kuma ba zai gajiya da Najeriya ba don daukakarsa,” gwamnan ya kara da cewa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a daren Asabar yayin wata liyafar cin abincin dare da aka shirya ta masu ruwa da tsaki a matsayin wani bangare na ayyukan bikin ranar Dimokiradiyya ta 12 ga Yuni wanda aka gudanar a gidan Gwamnatin Rayfield da ke Jos.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here