Gwamnan Jahar Bauchi ya Kaddamar da Shirin Bada Jari ga Matasa da Mata
Gwamnan Bauchi ya ware kimanin bilyan biyu don tallafawa mata da matasa.
An sa wannan shiri suna ‘ Shirin karfafa mutane da samar da aikin yi na Kaura’.
Wannan ya biyo bayan kaddamar da sabon sansanin jin dadin alhazai da gwamnan ya kaddamar Gwamnan jahar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya kaddamar da shirin bada jari wa mata da matasa karkashin shirin gwamnatinsa na KEEP.
Wannan na kunshe cikin jawabin da Legit ta samu daga Lawal Muazu Bauchi mai tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani.
Ya ce yayin bikin mika kayyakin da suka hada da jari, motoci da babura, injin markade da sauransu wa al’umar kananan hukumomin Gamawa da Zaki, gwamnan yace gwamnatinsa ta ware kimanin naira biliyan daya da miliyan dari biyar don bada jari da horaswa kan sana’oin hannu a fadin jaha.
Read Also:
Yace gwamnatinsa ta tsara kaddamar da rabon a wannan rana da ake bikin ranar dimokradiyya a Najeriya don nuna muhimmancin da matasa ke da shi a fannin shugabanci.
A cewar Gwamna Bala, shirin bada jari na KEEP zai tallafawa gwamnati wajen yaki da zaman kashe wando tsakanin al’uma musamman mata da matasa kuma tuni gwamnatin ta dauki nauyin horas da matasa kimanin dubu biyu kan noma da sana’oin hannu.
Ya yabawa al’umar kananan hukumomi biyun kan goyon bayan gwamnatin sa wajen gina sabuwar jahar Bauchi inda yace shirin za’a fadada shi zuwa dukkanin kananan hukumomi ashirin dake fadin jaha.
Saura da suka yi jawabi yayin bikin sun hada da shugaban jam’iyyar PDP ta jaha Alhaji Hamza Koshe Akuyam, Uwargidan Gwamna Hajiya Aisha Bala Muhammad, Yan majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar Gamawa da Zaki, Auwal Jatau da Madaki Gololo dukkanin su yabawa gwamnan suka yi kan shirin da suka bayyana da matakin inganta tattalin arziki da yaKi da talauci tsakanin al’uma.