Asari Dokubo ya Bayyana Yadda Femi Fani-Kayode ya Hada Shi da Shugaban IPOB

 

Tsohon kwamandan tsagerun Neja Delta, Mujahid Asari Dokubo, ya bayyana yadda Nnamdi Kanu ya turo masa.

Fani-Kayode Kamar yadda Dokubo ya bayyana, ya ce sun hadu da tsohon ministan sufurin jiragen saman a gidan gwamnatin Bayelsa.

Nnamdi Kanu ya tura Fani-Kayode domin ya tabbatar da hadin kan mambobin IPOB da na Neja Delta domin samun Biafra.

Tsohon kwamandan tsageru, Mujahid Asari Dokubo, ya bayyana yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya hada shi da Nnamdi Kanu, shugaban IPOB.

A wani bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta, Asari Dokubo ya kwatanta Kanu da barawo kuma ya sha alwashin maganinsa.

Ya zargi Kanu da samun riba da fafutukar Biafra tunda bashi da takamaiman aikin yi, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce ya karba Fani-Kayode a gidan gwamnatin jahar Bayelsa dake Yenagoa kuma sun yi magana kan yadda IPOB zasu hada kai da tsoffin tsageru.

“Ya ku ‘yan uwana ‘yan Biafra, kun ji muryoyin ‘yan ta’adda. Mun tambaya wadanda suka tara kudi amma ana ce mana India da Rasha, haka ne ake kididdigar kudin da aka kashe? Haka toh Biafra za ta kasance karkashin Nnamdi Kanu.”

“Dan ta’adda mai suna Nnamdi Kanu yayi ikirarin cewa an turo min kudi ta wani Omiomio. Ya ce an kawo min kudi har naira miliyan 20 a Cotonou.

“Muna jiransu su kawo shaida. Sun je Cotonou sun same ni, na basu masauki kuma na ciyar dasu. Basu kawo min ko sisi ba.

Akwai mutane daga wasu bangarorin Niger Delta, ba Ijaw kadai bane. Sun ci abincina kuma na biya musu wurin kwan, babu kobo da suka kawo.

“Na biya kudin asibitin mambobin IPOB a wurare daban-daban da suka samu rauni.

Na sadaukar da rayuwata, na tura lauyoyi inda aka tsaresu domin kokarin fitar dasu.

Mutane da yawa sun shaida hakan, amma Nnamdi Kanu barawo ne tunda yayi tunanin zai iya magana duk yadda ya so.

“Da farko, ina son tambayar Nnamdi Kanu, na taba tuntubarka? Kaine ka neme ni.

Mutum na farko da ka turo min shine Fani-Kayode. Ya zo kuma yace akwai bukatar mu hada kai.

Ban san kuma wanda ya nema a kasar Ijaw ba amma ni dai an same ni a gidan gwamnatin Bayelsa kuma daga nan muke magana da shi,” cewar Dokubo kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here