Gwamnonin Jam’iyyar PDP Sunyi ALLAH-Wadai da Bashin da Ake Bin Najeriya

 

“Ya kamata a ranto kudi saboda dalilai masu amfani, bashin da ake bin Najeriya a yanzu na sama da Naira tiriliyan 36 ya bayyana a fili mara amfani mai dorewa ga kudin shigar mu da GDP.

“Bai kamata mu dora wa karni masu zuwa nauyin bashi ba. Bashin da gwamnatin APC ke ci idan ba a yi hankali ba zai kai Najeriya ga fatarar rugujewa, ”sanarwar da aka fitar a karshen taron ta karanto wani sashi.

Gwamnonin sun yi Allah-wadai da cewa bashin da ake bin Najeriya tare da sama da 80% na alawus din da aka kashe wajen biyan bashi yana ta kara hauhawa kuma ya zama abinda ba za a iya shawo kansa ba.

Sun bayyana cewa duk nasarorin da gwamnatin PDP ta samu a lokacin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo lokacin da kasar ta fita daga bashin da kasashen waje ke bin ta duk yanzu ya rushe.

Gwamnonin sun zargi wannan gwamnati da karbar bashi don wasu abubuwa marasa kyau, suna masu jaddada cewa irin wannan matakin abin kunya ne.

Gwamnonin PDP sun yi watsi da tsarukan CBN da ayyukanta Legit ta gano cewa, gwamnonin sun y watsi da tsarin aiki na Babban Bankin Najeriya (CBN) wanda suke ikirarin suna aiki ne a matsayin gwamnati mai zaman kanta-a cikin-gwamnati.

“Yanayin da CBN ke kirkirar kudi, ta yanke shawarin nawa za a kashe, a kan abin da za a kashe shi ba tare da wani tsari na sarrafawa ko sa ido ba hakan ya saba wa tsarin mulkinmu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here