Bayan Tube Rawanin Basarake: Kotu ta Umarci Majalisar Sarakunan Gargajiya da su Hanzarta Fara Bin Tsarin Samar da Wani Sarkin
Kotun koli ta Najeriya, ta tube rawanin babban basarake Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V wanda shi ne Obong na masarautar Calabar.
An gano cewa, an dinga tafka shari’ar tun shekarar 2008 wacce tayi daidai da shekaru 15 bayan nada sarkin kuma ga hate karagar mulkin.
An gano cewa, ba ya cikin wadanda aka zaba a karon farko kafin a fara tantance wadanda aka zaba domin hawa karagar mulkin.
Calabar – Kotun koli ta tuge Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V, mai sarautar Obong na Calabar, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Read Also:
A hukuncin da Jastis Mohammed Lawal Garba, kotun ta umarci masu nada sarakuna da majalisar sarakunan gargajiya da su hanzarta fara bin tsarin samar da wani Obong na Calabar.
Kotun ta yanke hukuncin cewa a yi zaben sabon sarkin dogaro da kundin tsarin fadar na 2002.
Tsohon Ministan kudin karkashin mulkin Janar Sani Abacha, Etubom Anthony Ani da wasu a kara mai lamba HC/102/2008 wacce shugaban lauyoyinsu Joe Agi, SAN ya shigar, Otu da sauran a matsayinsu na mambobin majalisar sarakunan gargajiya na kudancin Calabar da yin magudi a tsarin tantance sabon sarkin.
Kotun tayi umarnin cewa:
“Wanda ake kara na farko Etubum Ani wanda ya amsa cewa ba ya cikin wadanda aka fara zabe domin tantancewa yayin zaben sabon sarkin kuma hakan yasa bashi da damar samun kuri’a ko daya.
“Mai daukaka kara na farko Abasi Otu a gargajiyance ya cancanta samun kuri’u.”
Don hakan kotun daukaka kara da soke tsarin da aka bi aka samar da Etubum Ani matsayin ‘dan takarar.