Champions League: Bayern Munich ta Doke Barcelona 3-0
Thomas Muller da Robert Lewandowski sun ci wa Bayern Munich 3-0 a gasar Champions League a karawar da ta doke Barcelona a Camp Nou ranar Talata.
Kungiyar Jamus ta fara cin kwallo ta hannun Muller kuma na bakwai da ya zura a ragar Barcelona a wasa shida da ya kara da ita.
Lewandowski ne ya ci na biyu kuma na 74 da ya zura a raga a Champions League daga baya ya ci na biyu kuma na uku a karawar sannan na 75 jumulla a gasar ta zakarun Turai.
Read Also:
Barcelona wadda ta buga wasan a karon farko ba tare da Lionel Messi ba ta kasa kai wani harin da zai sa ta zare koda kwallo daya ne a karawar.
Messi wanda ya ci kwallo 120 a Champions League a Barcelona shine na biyu a tarihin yawan zura kwallaye a raga, bayan Cristiano Ronaldo na Manchester United mai 136 jumulla.
Lionel Messi ya koma Paris St Germain a bana da taka leda, bayan da Barcelona ta fada matsin tattalin arziki da ta kasa tsawaita kwantiragin kyaftin din Argentina.
Ronaldo shine ya ci wa United kwallon da Young Boys ta doke kungiyar Old Trafford da ci 2-1 ranar Talata a Switzerland.
Ranar 14 ga watan Oktoban 2020 Bayern Munich ta doke Barcelona 8-2 a Porto a wasan daf da na kusa da na karshe da suka yi karawa daya don gudun yada cutar corona.