Hanyar Kaduna Zuwa Abuja: ‘Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Fulanin Bungudu Dake Zamfara, Hassan Attahiru

 

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace sarkin Fulanin Bungudu, da ke jahar Zamfara a arewacin Najeriya, mai martaba Alhaji Hassan Attahiru.

Ƴan bindigar sun sace sarkin ne kan hanyarsa daga Kaduna zuwa Abuja, kamar yadda ɗaya daga cikin ƴaƴansa da kuma basaraken masarautar Zannan Bungudu Hon Abdulmalik Zubairu ya tabbatarwa BBC.

Bayanai sun ce an kashe ɗaya daga cikin jami’in ƴan sanda a musayar wutar da ƴan bindigar suka yi jami’an tsaron da ke tare da sarkin cikin mota a hanyar Abuja.

Sarkin yana cikin sarakunan Zamfara masu daraja ta ɗaya.

Babu dai wata sanarwa daga rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, yankin da al’amarin ya faru.

Sace sarkin wani babban ƙalubale ne musamman a daidai lokacin da aka ɗauki mataki na toshe layukan sadarwa da hana cin kasuwannin mako domin maganin ƴan bindiga masu kai hare-hare- da satar mutane.

Karin bayani na tafe…

guest blog writing services

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

2 COMMENTS

  1. Lalle na shai’da arewa agenda tana daya daga cikin manyan kafafen sadarwa a fadin kasar nan,duba da irin korinda sukeyi,ba dare babu rana,Allah yakarawa arewa ageda daukaka,Allah yasa tazama ta daya a fadin kasar nan tamu,Amin….

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here