Hukumomi Sun Fara Bincike Kan Rushewar Gini Mai Hawa Bakwai a Legas
Hukumomi a Najeriya sun ce suna bincike kan wani gini mai hawa bakwai da ya rushe wanda ake aikinsa a jihar Legas.
An ceto mutum bakwai daga cikin ɓaraguzan ginin kuma tuni aka garzaya da su asibiti.
Waɗanda suka jikkatan duka masu aikin ginin gidan ne. Sai dai ya zuwa yanzu babu rahoton rasa rai a lamarin.
Read Also:
Babu wanda ya san sanadin rushewar ginin, sai dai shugaban hukumar ba da agajin gaggawa na jihar ya zargi wata katuwar mota da ta shiga cikin gidan da ake ginawa.
Hukumomi sun ce babu wanda ya bai wa masu ginin izinin ginin a wajen.
Wani bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta ya nuna yadda ginin ya rushe.
Wannan lamari da ya faru ne a yammacin ranar Laraba a yankin rukunin gidaje na Banana Island.