Jerin Jiga-Jigan Ƴan Majalisa da ke Neman Shugabancin Majalisar Dattawa

 

Ƴan majalisar dattawa da dama sun shiga cikin jerin masu neman shugabancin majlisar dattawa ta 10.

Tun kafin a rantsar da sabuwar majalisar dattawan ta 10, ƴan majalisu sun fito fili sun nuna maitar su don samun shugabancin majalisar.

Majalisar dattawan ta 10 zata fara ne aiki ne a watan Yuni bayan an rantsar da Asiwaju Bola Tinubu.

FCT, Abuja – A yayin da ake shirin rantsar da majalisar dattawa ta 10, zaɓaɓɓun ƴan majalisa da dama sun fara neman kujerar shugabancin majalisar.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, za a rantsar da sabuwar majalisar ne a cikin watan Yunin 2023, bayan an rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Majalisar dattawan ta 10 zata cika ne da ƴan majalisun da suka fito daga jam’iyyun All Progressives Congress (APC), Peoples Democratic Party (PDP), Labour Party (LP) da New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Sauran jam’iyyun sun haɗa da Social Democratic Party (SDP), All Progressives Grand Alliance (APGA) Young Peoples Progressive Party (YPP).

Tuni dai aka fara neman shugabancin majalisar dattawan tun kafin a rantsar da ita.

Ana kyautata zaton cewa zaɓen sabon shugaban majalisar dattawan zai zo ne ta hanyar tsarin karɓa-karɓa na jam’iyyar APC mai mulki.

Jaridar Blueprint tace kakakin majalisar dattawa, Sanata Ajibola Basiru, ya bayyana cewa akwai yiwuwar jam’iyyar APC ta saki jadawalin tsarin shugabancin majalisar dattawa ta 10 bayan azumin Ramadan.

Sanata Basiru ya bayyana hakan ne a safiyar ranar Laraba, yayin wata tattauna da gidan talbijin na Channels tv a shirin su mai suna Sunrise Daily.

Ga jerin ƴan majalisar da ke neman shugabancin majalisar dattawa ta 10:

1. Senator Jibrin Barau (Kano ta tsakiya).

2. Sani Musa (Niger ta Gabas).

3. Orji Kalu (Abia ta Arewa).

4. GodsWill Akpabio (Akwa-Ibom ta Arewa maso Yamma).

5. Senators Osita Izunaso (Imo ta Yamma).

6. Peter Ndubueze (Imo ta Arewa).

7. Abdul’Aziz Yari (Zamfara ta Yamma)

8. Ahmad Lawan (Yobe ta Arewa).

9. Ali Ndume (Borno ta Kudu).

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here