Ofishin Binciken Hatsari ya yi Watsi Akan Binciko Lamarin Fashewar Tayar Jirgin Sama a Jahar Kwara

 

Ofishin binciken hatsari ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar kin binciko lamarin da ke kewaye da fashewar taya a Filin jirgin saman Ilorin.

Wani mai magana da yawun ofishin ya karyata rahotannin da ke nuna cewa wani mummunan hatsari ya faru a filin jirgin.

Har yanzu Hukumar Filin Jirgin Sama ta Najeriya ba ta fitar da wani bayani a hukumance game da lamarin ba.

Ofishin Binciken Hadari (AIB) ya yi watsi da rahotannin da ke ikirarin cewa wani jirgin sama na daya daga cikin manyan kamfanonin jiragen saman kasar ya fadi a kan titin jirgi a filin jirgin saman Ilorin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tayoyin jirgin sun tarwatse bayan ya sauka a filin jirgin saman Ilorin na jahar Kwara a ranar Juma’a, 23 ga watan Yuli.

Jaridar ta ce lamarin ya faru ne lokacin da jirgin ke rangaji zuwa wajen sauka a filin jirgin.

Sai dai, mai magana da yawun kamfanin jirgin, Stanley Olise, ya shaida wa jaridar cewa an gyara tayar sannan kuma aka dauke jirgin daga filin tashin.

Har ila yau da yake tabbatar da faruwar lamarin, Ofishin Binciken Hatsari, hukumar bincike da ke kula da dukkan hadurra da abubuwan da suka shafi jirgin sama a Najeriya, ta ce babu wani hatsarin jirgin sama.

AIB ya tabbatar da fashewar taya a yayin sauka.

Mai magana da yawun kungiyar ta AIB, Tunji Oketumbi, ya bayyana cewa tayar jirgin ya fashe a yayin sauka.

Ya ce:

‘’Eh. Ya faru jiya. Masu bincike na AIB sun auna lamarin kuma sun yanke shawarar ƙin yin bincike. An saki jirgin ga matukin.

“Jinkirin da FAAN (Hukumar filayen jiragen saman Najeriya) da Airpeace suka yi wajen bude filin jirgin ya kasane saboda farfadowar jirgin sama daga wajen tashi.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here