Kotu ta Bada Umarnin Sakin Zakzaky da Matarsa

Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, a yau 28 ga watan Yuli, an yanke hukunci kan Zakzaky da matarsa, inda tuni aka wanke su daga zargi.

A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waɗanda ake zargin daga zargi takwas da gwamnatin Jahar Kaduna ta gabatar mata, in BBC Hausa.

Rahoton ya ce tuni bayan yanke hukuncin aka zarce da Zakzaky zuwa gida nan take, kuma ba a tsaya sauraran ‘yan jarida ba.

Tun farko, ba a ‘yan jarida da sauran jama’a damar shiga zauren kotun ba.

A cewar gidan talabijin na Channels, zaman sauraran shari’ar ya shafe akalla sa’o’i takwas kafin cimma wanke malamin da matarsa, tare da ba da umarnin sakinsu.

Karin bayani na nan tafe…

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here