Saurin Karewar Data: Hukumar NCC ta Fara Binkice Akan Haka

Bayan rage farashin Data, yan Najeriya sun koka kan saurin karewarta.

Hakazalika anyi korafe-korafen kwashe wa mutane kudi waya.

Hukumar NCC ta lashi takobin gano gaskiyar abinda ke faruwa.

Hukumar kula da sadarwan Najeriya NCC ta bayyana cewa ta kaddamar da bincike kan kararrakin da ake shigarwa kan saurin karewan Data da kwashewa mutane kudi a waya.

Shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Danbatta, a ranar Alhamis ya bayyana haka a wani taron bashi lambar girma da mujallar MoneyReport ta bashi a matsayin jarumin 2020 a Abuja.

Danbatta ya ce hukumar na iyakan kokarinta wajen ganin cewa kamfanonin sadarwa ba sa cutan jama’a.

Ya ce ta wannan bincike na hukumar ke gudanarwa, “za’a gani takamammen dalilin da yasa Data ke saurin karewa da mutane ke fuskanta da kuma kwashewa mutum kudi da bai dace ba.”

“Mun bayyana cewa duk da rage farashin data, sai an cigaba da binciken kuma an nunawa kamfanonin sadarwa sakamakon binciken,” Danbatta yace.

Danbatta ya yi kira ga yan Najeriya suyi hakuri yayinda ake gudanar da binciken saboda hukumar za ta tabbatar da cewa kamfanonin sun yi abinda ya dace domin jin dadin kwastamomi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here