Hukumomin Birtaniya Sun Ayyana Kisan ɗan Majalisa a Matsayin ta’addanci
Bayanai sun nuna cewa mutumin da ake tsare da shi kan kisan dan majalisar Birtaniya, David Amess, a ranar juma’a ya taɓa halartar shirin gwamnati na yaƙi da tsattsauran ra’ayi.
Sai dai babu sunan matashin mai suna Ali Harbi Ali a cikin jerin waɗanda jami’an tsaron kasar ke sanya wa ido saboda zargin ta’addanci.
Read Also:
Wakilin BBC ya ce a hukumance a daren jiya ne aka ayyana harin a matsayin na ta’addanci.
Tun da fari an bayyana cewa makasudin kai harin na da alaka da tsattsauran ra’ayin Musulunci.
An tsare matashin mai shekara 25 ɗan Birtaniya kuma dan asalin Somalia a inda ya daba wa dan majalisar wuka.
Jaridar Sunday Times ta yi hira da mahaifin Mista Ali, inda ya ce har yanzu yana cikin tashin hankali da kaduwa kan abin da dansa ya aikata.