Covid-19 Karo na 3: Najeriya ta Biya Kudin Rigakafin Corona Guda 30m Daga Amurka – Dr Osagie Ehanire

 

Gwamnatin tarayya ta ce adadin mutanen da suka kamu da COVID-19 karo na uku bai kai a kafa dokar kulle ba.

Dr Osagie Ehanire, ministan lafiya, ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai.

Ministan yace Najeriya ta biya kudin alluran rigakafin J&J guda milyan 30 daga Amurka.

Fadar Aso Rock, Abuja – Gwamnatin tarayya ta ce bata shirya kafa wani sabon dokar kulle ba duk da dawowar cutar COVID-19 a fadin tarayya.

Channels TV ta ruwaito cewa ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 12 ga Agusta, a taron mako-mako na hira da manema labarai a fadar shugaban kasa, Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa Ministan yace adadin mutanen da suka kamu bai kai a kakaba sabuwar dokar kulle ba.

A ranar Laraba, 11 ga Agusta, hukumar dakile yaduwar cututtuka NCDc ta cewa sabbin mutane 790 suka kamu da cutar Korona.

Wannan shine adadi mafi yawa cikin watanni shida.

Wannan sabuwar yaduwar da cutar keyi ya biyo bayan bullar sabuwar launin cutar da aka fi sani da ‘Delta’.

Najeriya ta biya kudin rigakafin COVID-19

Ehanire ya kara da cewa bayan rigakafin da Najeriya ta nema kyauta, Najeriya ta biya kudin kwayoyin rigakafin Johnson&Johnson guda milyan 30.

A cewarsa, tunda farashin allurar ya sauka yanzu, ana sa ranar sayan guda milyan 40.

Ehanire yace tuni rigakafin Johnson&Johnson guda 176,000 sun isa Najeriya yayinda sauran ke hanyar zuwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here