Kungiyar Boko Haram ta Fadi Dalilinta na Kai Hare-Hare a Fadin Kasar nan

 

A yayin da ‘yan Boko Haram ke kai miyagun hare-hare a Geidam, sun raba wasiku ga mazauna wurin.

Kamar yadda wasikun suka bayyana, ‘yan Boko Haram sun ce Jihadi suke tabbatarwa a kan sojojin Najeriya.

Kungiyar ta’addancin tace ta bayyana cewa hatta wadanda ke goyon bayan sojojin Najeriya sai sun ga bayansu.

Bayan miyagun hare-haren da ‘yan Boko Haram suka kai a garin Geidam dake jahar Yobe a ranar Juma’a, 23 ga watan Afirilu, sun raba wasika ga mazauna yankin yayin harin.

A yayin bada dalilin da yasa suke kaiwa ‘yan Najeriya hari, kungiyar ‘yan ta’addan a wasikar ta bayyana cewa Boko Haram ta zo yin jihadi ne da rundunar sojin Najeriya.

A karin bayani, an rubuta wasikar a harshen Hausa kuma a wasikar an jaddada cewa sun fito ne domin halaka duk wani wanda ke hana Jihadi ko kuma yake aiki tare da hukumar tsaron Najeriya.

Vanguard ta samu wasikar da ‘yan Boko Haram suka raba a yankin, wanda a takaiace yace, “Muna fadan Jihadi ne, muna kuma harar rundunar soji, masu hada kai dasu da kuma duka wani wanda zai hana su daga yin Jihadi.”

“An bada wasikar ne a rubuce a harshen Hausa kuma na raba su ga mazauna Geidam a yammacin Juma’a kafin su fara aiwatar da harin,” wata majiyar ta bayyana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here