An Gwabza Tsakanin Sojojin Kasar Chadi da ‘Yan Ta’adda

 

‘Yan ta’adda masu da’awar Jihadi sun kai hari kan wasu sojojin kasar Chadi inda suka hallaka 12.

An ruwaito cewa, an hallaka ‘yan ta’addan 40, saura kuma sun gudu sun bar gawarwakin ‘yan uwansu.

Fada tsakanin sojojin na Chadi da ‘yan ta’addan ya faru ne da wayewar garin yau, ranar Talata Fadan da aka gwabza tsakanin sojoji da masu da’awar jihadi a yankin tafkin Chadi a ranar Talata ya yi sanadiyyar rayukan ‘yan kasar ta Chadi akalla 12, kamar yadda wani gwamnan lardin ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP.

Mahamat Fadoul Mackaye ya ce an kuma kashe mayakan 40 bayan harin da aka kai kan wani sansanin sojoji a yankin na fadama da kungiyoyin jihadi da suka hada da Boko Haram da ke Najeriya da kuma wani reshe na kungiyar ISWAP suka yi a baya-bayan nan.

“Dakarun tsaron sun mai da martani mai karfin gaske don fatattakar abokan gaba, wadanda suka bar gawarwaki 40 da makamai, amma muna bakin cikin rashin sojoji 12,” in ji Mackaye ga AFP ta wayar tarho.

‘Yan Boko Haram da ISWAP suna kai wa sojoji hari har da fararen hula a yankunan Chadi arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar ISWAP ta balle daga kungiyar Boko Haram a shekarar 2016 ta kuma zama kungiyar da ta fi karfi, ta fara kai hare-hare a kan sansanonin soja da kuma yi wa sojoji kwanton bauna yayin sace matafiya a wuraren binciken bogi.

Fadan na ranar Talata ya faru ne da wayewar gari tsakanin garuruwan Ngouboua da Kaiga, wadanda ke da nisan kilomita 100 arewa da babban birnin N’Djamena, in ji wani babban jami’in jami’an tsaro, wanda ya nemi a sakaya sunansa. Kakakin rundunar sojojin Chadi, Janar Azem Bermandoa Agouna, ya tabbatar da afkuwar harin amma ya ki bada adadin wadanda suka rasa rayukansu lokacin da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tuntube su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here