ƙungiyar Boko Haram ta Kashe Sojoji da Dama a Borno
Wasu maharan da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram ne sun kashe sojojin Najeriya da dama, yayin da wasu da dama suka jikkata a jihar Borno da ke arewacin Najeriya.
Al’amarin ya faru ne a lokacin da ƴan bindigan suka kai hari kan sansanin soji da ke Wajirko a Damboa da sansanin soji na Wulgo a Gamboru Ngala da yammacin ranar Litinin.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa a yayin harin kuma an kashe wasu daga cikin mayakan na Boko Haram.
Read Also:
Haka kuma wasu rahotanni na ce kwamandan sojin da ya kai ɗauki ya taka nakiya da ta fashe, lamarin da ya janyo karin jikkata wasu da ma rasa rayuka.
Sansanin na Wulgo na bakin iyakar jamhuriyyar Kamaru, kuma yana ɗauke da sojin haɗaka na Najeriya da ƙasar ta Kamaru.
A baya-bayan dai ana ci gaba da samun ƙarin hare-haren daga ƙungiyar bayan an samu lafawarsu na wani lokaci.
Tun a shekarar 2009 aka fara rikicin Boko Haram a arewa-maso-gabashin Najeriya, rikicin da ya kai ga mutuwar kimanin mutane 40,000, yayin da wasu miliyan biyun suka tsere daga muhallansu.