Gwamnatin Borno ta Karbi Bakuncin Sojojin Kamaru

Gwamnan jihar Borno, ya tarbi sojojin Kamaru a ranar Alhamis.

Ya bukaci taimakonsu don kawo karshen ta’addanci a jihar.

Yana so su hada karfi da karfe da sojin Najeriya don taimakon yankinsa.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya tarba sojoji daga Kamaru a ranar Alhamis. Sojojin sun isa gidan gwamnati da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

A taron, gwamnan ya bukaci sojojin Kamaru da su taimaka wurin kawo karshen ‘yan ta’addan Boko Haram, jaridar Punch ta wallafa.

Kwamandan rundunar soji na 4, Janar Saly Mohammadou, ya jagoranci sojojin Kamaru zuwa gidan gwamnatin.

Kwamandan Sector 1 Multinational joint Task Force, Janar Bouba Debekreo, Birgediya janar Essoh Jules-Cesar, GOC 7 Div Bridgdier, Janar AK. Ibrahim da sauransu ne suka raka su.

A cewar Zulum, sojojin Kamaru sun zo Najeriya ne don su taya sojojin Najeriya wurin yaki da ta’addanci a wuraren tafkin Chadi.

Kamar yadda yace, “Mafi yawan mutanen Kamaru da Najeriya suna da al’adu iri daya. Duk da rashin tsaron ya shafin yankin tafkin Chadi, kuma hakan ya shafin tattalin arzikinmu. Shiyasa yakamata mu taru mu yaki rashin tsaro.

“Batun siye da siyarwa tsakanin iyaka, dukanmu mun san Banki. Muna iyakar kokarin ganin mun kara bude kasuwar Banki da kuma titunan Banki. Yanzu ya kamata mu bayar da hadin kai wurin kawo karshen rashin tsaro, don jama’a su samu damar yin tafiye-tafiye yadda suka saba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here