Gwamnatin Jahar Borno ta Dakatar da Shugabannin Makarantar Kimiyya ta Ramat da ke Maiduguri
Gwamnan jahar Borno, ya dakatar da shugabannin makarantar kimiyya ta Ramat da ke Maiduguri, na tsawon watanni shida.
Zulum ya dauki wannan mataki ne sakamakon gani da yayi komai na makarantar ya mutu murus a yayin da ya kai ziyarar bazata.
Ya kuma umurci kwamishinan ilimi na jahar, Dr. Babagana Mallumbe, da ya karbi ragamar harkokin Makarantar nan take sannan ya saisaita abubuwa cikin gaggawa.
Gwamna Babagana Zulum ya dakatar da dukkanin shugabannin kwalejin kimiyya ta Ramat da ke Maiduguri, na tsawon watanni shida.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Zulum ya kasance dalibin kwalejin kimiyyar daga shekarar 1986 zuwa 1988.
Ya sami difloma a bangaren Injinyan Noma kafin ya koma makarantar a matsayin shugaba daga 2011 zuwa 2015.
A yayin ziyarar bazata da ya kai, gwamnan ya yi mamakin ganin cewa dakunan bitar aiki da na gwaje-gwaje ba sa aiki, yayin da ‘makarantar ta mutu murus’.
Gwamnan ya ziyarci makarantar da misalin ƙarfe 9:00 na safe sannan ya gano cewa ba a amfani da yawancin dakunan gwaje-gwajen, inda ya-na suka rufe wasun su sannan ga beraye suna yawo saboda rashin kulawa.
Read Also:
Bayan tantance wurin, Zulum ya umarci kwamishinan manyan makarantu, kimiyya, fasaha da kirkire -kirkire na jahar, Dr. Babagana Mallumbe, da ya karbi ragamar harkokin Makarantar nan take, Daily Trust ta kuma rawaitowa.
Ya ce:
“Ni a iya sanina, wannan Kwalejin ta mutu. Babu abin da ke aiki. Dakunan bitar aiki sun tashi aiki, dakin bitar aikin gona ba ya aiki, haka nan cibiyar sana’o’i ba ya aiki.
“Makarantar tana fuskantar dubban matsaloli, kama daga rashin kudi da jajircewa. A matsayina na tsohon ɗalibin wannan kwalejin, tsohon shugaba, ina da riko da ɗabi’a a wannan kwalejin. Insha’Allah, ba zan bari wannan kwaleji na kimiyya ta lalace a lokacin da nake a matsayin Gwamnan Jahar Borno ba. Zan yi duk abin da zan iya don tabbatar da aikin wannan cibiya insha Allah.
“Na umarci Kwamishinan Ilimi da ya karbi ragamar harkokin makarantar na watanni shida masu zuwa. Ma’aikatar ta tabbatar da ganin cewa an dawo da dukkan bita da dakunan gwaje -gwaje bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.
“Sannan a gaggauta dawo da cibiyar sana’o’i don amfani da ita. Lokacin da nake a matsayin shugabar makarantar, cibiyar sana’o’i tana samar da akalla teburi da kujeru 10,000 zuwa 20,000 kowane wata. Mun samar da gadajen asibiti.”
Gwamnan ya yi ganawar sirri tare da manyan manajojin Kwalejin.