Gwamnatin Jahar Borno ta Gana Kan ‘Yan Boko Haram da Suka Mika Wuya

 

Shugabannin al’umma daga kowane ɓangare na jahar Borno sun gana kan mayakan Boko Haram da suka mika wuya.

Taron wanda ya kunshi shugabannin siyasa, sarakuna da na addinai ya fidda matsaya kan lamarin.

A sanarwar da suka fitar bayan taron, sun amince da tubabbun yan Boko Haram amma bisa wasu sharuddai.

Borno – Shugabannin al’umma a jahar Borno, ranar Lahadi, sun amince a mai da mayakan Boko Haram da suka mika wuya cikin mutane, kamar yadda premium times ta rawaito.

Shugabannin sun amince da haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da gwamnatin Borno ta shirya domin tattauna matsalar tsaro da ake ciki a jahar.

Gwamnatin Borno ta tabbatar da cewa aƙalla yan kungiyar Boko Haram 3,000 ne suka mika wuya ga rundunar sojoji.

Gwamna Babagana Umaru Zulum, wanda ya jagoranci taron, yace bayan mutum 3,000, akwai karin mutum 900 da suka mika wuya ga jami’an Kamaru.

Zulum yace taron masu ruwa da tsaki ya zama wajibi ne biyo bayan yadda ake kace-nace kan yawaitar mika wuyan mayakan Boko Haram.

Zulum yace gwamnati tana bukatar saka masu ruwa da tsaki na jahar domin ɗaukar matakin da ya dace kan mayakan da suka aje makamansu.

Su waye suka halarci taron?

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da, manyan jami’an gwamnati daga mataki daban-daban, sarakuna, shugabannin addinai, jami’an tsaro da kuma wasu daga cikin mutanen jahar.

A karshen taron, sun tsaida matsayar amincewa da tubabbun yan ta’addan, amma sun bada sharuddan da za’a cika kafin mayakan su shiga cikin al’umma.

Legit.ng Hausa ta gano cewa sanarwar da suka fitar bayan taron tana ɗauke da sa hannun Antoni Janar na jahar, Kaka Shehu Lawan.

Wane sharudda suka kafa kafin amsar tubabbun?

Masu ruwa da tsakin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahar Borno cewa: “Su jagoranci lamarin mayakan da suka mika wuya da kulawa sosai kuma da bin ka’idoji da dokoki.”

Taron ya jaddada bukatar “Bincike da ɗaukar bayanan mayakan Boko Haram domin gudun sako mutane masu hatsari cikin al’umma.”

Hakanan shugabannin sun yi kira ga mazauna Borno “Su yi amafani da damar samun ilimi da gwamnatin Borno ta kirkiro musamman saka ƴaƴansu makaranta domin gudun kada a canza musu tunani.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here