Gamnatin Borno ta Dauki Nauyin Karatun Yaran CJTF da Boko Haram ta Kashe Tun 2013

Ya yi alkawarin N180m, buhuhunan hatsi da kwalayen abinci 27,000 ga mayaka 9000

Gwamnan ya shirya tsarin taimakawa matasan jami’an sa kai da aka kashe – Ya mika godiyar al’ummar Borno ga iyalan yan sa kai bisa sadaukarwan da sukayi Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince daukan lauyin karatun yara marayu, wadanda iyayensu suka kasance yan Civilian JTF, mafarauta da yan banga da suka rasa rayukansu a filin daga Boko Haram a shekaru bakwai da suka gabata.

Zulum ya kaddamar da asusun lamunin N50,000 ga ko wacce cikin matan wadanda suka rasa rayukansu a yakin Boko Haram sannan kuma a rabawa yan CJTF masu yakan Boko Haram 9000 dake fafatawa yanzu kudi N180m, buhuhuban hatsin da kwalayen abinci 27,000.

Gwamnan ya sanar da dukkan wadannan tallafin a ranar Laraba a Maiduguri, yayinda yake jawwabi ga yan sa kai 9,000 da ke yakan Boko Haram tare da Sojoji a Borno. An tara yan sa kan ne a cikin jami’ar jihar Borno. Kowanne daga cikin yan sa kai zai samu kudi N20,000, buhun shinkafa kilo 50, kwalin taliya daya da galan mai daya, kuma dukkan hakan bai cikin albashinsu na wata

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here