An Damke Sojojin da Aka Kama Suna Zabgan Matasan da Suka Saba Dokar Hana Fita

Hukumar Sojin saman Najeriya ta yi tsokaci kan zargin cin zarafi da take hakkin dan Adam da aka yiwa wasu jami’anta.

Hukumar ta yi Alla-wadai da abinda Sojojin suka yi – A cewar hukumar, abinda jami’anta sukayi ya sabawa ka’idojin da koyarwanta Hukumar Mayakan saman Najeriya ta damke wasi jami’anta dake aka gani a faifan bidiyo suna zabgan wasu matasa da suka saba dokar hana fita a jihar Osun.

A wani jawabi ranar Laraba, 28 ga Oktoba, ta shafinta na Tuwita, hukumar tace an damke hafsoshin ne bayan bidiyo ya nunasu karara suna zane mutane a garin Ilesha. Hukumar ta ce ba zata lamunci irin wannan abu ba saboda ba ta yarda take hakkin dan adam ba. Air Force ta ce dukkan abinda Sojojin sukayi ya sabawa koyarwanta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here