Borno: Dakarun Sojin Najeriya Sun Fatattaki ‘Yan Ta’addan da Suka Kai Hari
Rundunar Sojin Najeriya ta Army Super Camp sun mayar da harin da ‘yan Boko Haram suka kai Ngamdu da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno.
Read Also:
Sun samu nasarar ragargazar ‘yan ta’adda da maboyarsu a tsakanin dajin Sambisa, tsaunikan Mandara da tafkin Chadi – Yan Boko Haram sun dade suna kai farmaki a kananan hukumomin da ke jihar Borno, yanzu haka sun kashe fiye da mutane 30,000 A ranar Alhamis da yamma, rundunar Army Super Camp suka mayar da harin da ‘yan ta’adda suka kai Ngamdu da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno. HumAngle sun gano cewa ‘yan Boko Haram ne suka kai harin. Sun kai harin ne bayan kwanaki kadan da shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai yayi sintiri a dajin Ngamdu-Goniri a ranar 17 ga watan Oktoba. Ngamdu iyakar jihar Borno da jihar Yobe ne, kusa da dajin Alagarno. HumAngle ta sanar da harin da rundunar Operation Lafiya Dole ta kai Doksa, karamar hukumar Damboa a jihar Borno. Al’amura sun fara cabewa ne tun bayan sojoji sun fara kutsa kai da wani sabon shirin su na ‘Operation Fireball’ don kai hari ga ‘yan ta’addan da ke zagayen Timbuktu, tsakanin dajin Sambisa, tsaunikan Mandara da tafkin Chadi. Miyagun ‘yan ta’addan sun dade suna addabar Arewa maso gabas a Najeriya, wanda hakan ya janyo mutuwar fiye da mutane 30,000 da kuma bata da rasa gidajen fiye da mutane Miliyan 2
A wani labari na daban, hedkwatar tsaro tace Operation Lafiya Dole ta samu nasarar ragargazar ‘yan Boko Haram 4, kuma ta kwace bindigogi AK47 a hannunsu, yayin da suka je aiki kauyen Sawa dake karamar hukumar Nganzai dake jihar Borno. Kakakin rundunar sojin, John Enenche, ya sanar da hakan yayin da yake bayar da bayani a kan ayyukan da rundunar suka yi a ranar Alhamis a Abuja.