Dalilin da Yasa Buhari ya ki Magana a Kan Harbin Lekki

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanar sa dalilinta na yin shiru a kan harbe-harben Lekki.

Mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman a fannin yada labarai, Femi Adesina ya sanar da dalilin – Ya ce zai zama tamkar riga Malam masallaci ne domin ba a kammala bincike a kan lamarin ba Shugaban masa Muhammadu Buhari bai ce komai a man harbe-harben da aka yi wa masu zanga-zangar EndSARS a Lekki a ranar Talata ba a jawabin da yayi ga ‘yan Najeriya saboda baya son yayi riga Malam masallaci. Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun nuna damuwarsu a kan rashin maganar shugaban kasan ko jaje ga jama’ar da suka rasa rayukansu. Sun kwatanta hakan da ganganci da kuma rashin nuna kulawa
Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanar sa dalilinta na yin shiru a kan harbe-harben Lekki – Mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman a fannin yada labarai, Femi Adesina ya sanar da dalilin – Ya ce zai zama tamkar riga Malam masallaci ne domin ba a kammala bincike a kan lamarin ba Shugaban masa Muhammadu Buhari bai ce komai a man harbe-harben da aka yi wa masu zanga-zangar EndSARS a Lekki a ranar Talata ba a jawabin da yayi ga ‘yan Najeriya saboda baya son yayi riga Malam masallaci. Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun nuna damuwarsu a kan rashin maganar shugaban kasan ko jaje ga jama’ar da suka rasa rayukansu. Sun kwatanta hakan da ganganci da kuma rashin nuna kulawa.
Amma kuma, mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman a fannin yada labarai, Femi Adesina, wanda ya bayyana a shirin siyasarmu a yau a gidan talabijin na Channels, ya ce shugaban kasan bai samu cewa komai a kan harbin ba saboda ba a kammala bincike a kai ba.
Ya ce: “Hedkwatar tsaro ta fitar da takarda inda tace tana bincikar lamarin. Gwamnan jihar Legas ya kafa kwamitin bincike a kan abinda ya faru. “Toh don haka shugaban kasan bashi da ta cewa saboda zai zama tamkar riga Malam masallaci ne a kan binciken da ake yi. Bayan binciken ne zai yanke hukuncin magana a kai.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here