Kotu ta Yanke wa Tsohon Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya,Francois Bozize ɗaurin Rai-da-Rai

 

Wata kotu a Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga tsohon shugaban ƙasar, Francois Bozize.

An yanke wa Mista Bozize mai shekaru 76 – wanda a yanzu ke jagorantar ƙawancen ‘yan tawaye – hukunci ne a ranar Alhamis bisa tuhume-tuhume da suka haɗa da tawaye da kuma zagon ƙasa ga tsaro.

An kuma yanke wa fiye da wasu 20, ciki har da ’yan uwan Bozize biyu hukunci.

A shekarar 2003 ne Bozize ya ƙwace mulki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda shi kuma aka hamɓarar da shi shekara goma bayan da ya fara mulki.

lamarin da ya haifar da yaƙin basasa da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

A yanzu tsohon shugaban na zaune a Guinea-Bissau.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com