Garkuwa: An Ceto ɗaliba 6 na Jami’ar Tarayya da ke Gusau

 

An ceto shida daga cikin ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau waɗanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da su daren Juma’a.

Sai dai har yanzu babu tabbas kan yawan ɗaliban da maharan suka sace.

Ƴan bindigar waɗanda suka isa unguwar Sabon Gida da tsakar dare, sun rinƙa harbe-harbe kafin su yi awon-gaba da ɗaliban.

Jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar, Umar Usman ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai bayyana adadin ɗaliban da aka yi garkuwar da su ba.

Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi jigata daga ayyukan ƴan bindiga masu fashi da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Ko a cikin watan Fabarairun 2021, ƴan bindiga sun shiga makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a jihar, inda suka sace ɗalibai mata 317.

Haka nan ma a baya-bayan nan ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyukan jihar inda suka kashe mutane da dama tare da sace ƴan mata fiye da 30 a ƙaramar hukumar Maradun.

Maharan sun abka ƙauyukan Sakkiɗa da Janbako da rana tsaka, inda suka kashe mutum sama da 20 a Sakkiɗa tare da jikkata karin wasu.

Ita dai gwamnatin jihar ƙarƙashin gwamna Dauda Lawal, ta ce tana ɗaukar duk matakan da suka dace wajen shawo kan lamarin, sai dai ta sha alwashin cewa ba za ta taɓa yin sulhu da ƴan bindiga ba.

A baya dai gwamnatocin da suka gabata a jihar sun ɗauki matakai daban-daban, ciki har da na yarjejeniya da ƴan bindigar, sai dai har yanzu matsalar ta ci tura.

‘Mun ji hayaniyar mutane da harbe-harben bindiga’

Wani ɗalibin jami’ar ta FUG ya shaida wa BBC cewa tun a farko-farkon dare ne suka ji harbin bindiga, sai dai ba a jima ba abin ya lafa, inda daga baya kuma ƙarar bindigar ta sake tayar da su daga bacci.

Ya ce “A lokacin sai muka tashi muka riƙa kulle tagogi da kofofi saboda tsorata.”

Ya ƙara da cewa bayan haka ne sai suka rinƙa jin hayaniyar mutane “wata ƙila shi ne lokacin da suka tafi da ƴanmatan,” in ji shi.

Sai dai ya ce bai su samu ganin abubuwan da ke wakana saboda duhun dare.

Amma a cewarsa bayan wani lokaci sun ga kwambar motocin sojoji ta zo unguwar, inda aka ci gaba da jin ƙarar bindiga.

Ɗalibai da malamai sun ƙaurace

Waɗansu da BBC ta tattauna da su, waɗanda suka samu shiga harabar jami’ar da ke Gusau, sun ce abubuwa sun tsaya cak.

“Gaba ɗaya za a iya cewa duk wanda ke cikin jami’ar sun taru wuri ɗaya, babu wanda ke son ya je wani wuri, kuma ma babu mutane sosai, mutane kaɗan ne.” In ji ɗaya daga cikin waɗanda BBC ta zanta da su.

Ya ce da alama labarin harin ƴan bindigar ne ya sanya da dama daga cikin ɗalibai da kuma malamai suka ƙi shiga jami’ar da safiyar ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa ko a lokacin da ya shiga ginin ofososhin gudanarwa na jami’ar, yawancin su suna a kulle, kuma babu hada-hada ko gilmawar mutane kamar yadda aka saba.

Bugu da ƙari, an soke wasu daga cikin darussan da suka kamata a ce sun gudana da safiyar juma’a.

“Muna da lectures da safe, amma duk ba a yi ba.” In ji ɗaya daga cikin waɗanda suka tattauna da BBC.

Jami’an tsaro

Duk da dai babu tsattsauran matakan tsaro da aka ɗauka, amma da alamun akwai ƙarin jami’an tsaro da ke sintiri a kusa da jami’ar.

Waɗanda suka samu shiga harabar, sun bayyana cewa sai da jami’an tsaro suka tantance kafin a basu izini, kasancewar akwai jami’an tsaro da suka yi tunga a bakin ƙofar shiga jami’ar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com