BPE: Za a Saida Afam a Kan Kudi Naira Biliyan 105
Ana sa ran yau a kammala cinikin saida Afam Power Plant a Aso Villa.
Gwamnatin Tarayya za ta saida wa ‘yan kasuwa wurin samar da wutan.
Za a saida wa Transcorp PLC tashar lantarkin ne a kan Naira biliyan 105 Gwamnatin tarayya za ta samu Naira biliyan 105 daga saida wurin samar da wuta na Afam.
Vanguard ta fitar da wannan rahoto a yau da safe. Shugaban hukumar BPE mai alhakins saida kadarorin gwamnatin tarayya, Alex Okoh, ya shaida wa ‘yan jarida wannan a ranar 4 ga watan Nuwamba.
Alex Okoh ya ce za a karkare cinikin nan ne a fadar shugaban kasa na Aso Villa a birnin tarayya Abuja.
Read Also:
A cewar Mista Alex Okoh, duk da annobar COVID-19 da ta jagwula lissafi, hukumar BPE ta cigaba da gudanar da ayyukanta ba tare da gaza wa ba.
Okoh ya kuma karyata rahotonnnin da ke yawo cewa hukumar BPE ta yi awon gaba da wasu Naira biliyan 2.5 daga cikin kudin da aka saida PHCN.
BPE ta yi karin haske game da gaskiyar yadda lamarin ya ke:
“A ranar 25 ga watan Fubrairun 2014, BPE ta samu dama daga OAGF na samun alaka da kamfanin Aso Savings & Loans Plc., su ka adana N2.5bn a asusunsu.”
Shugaban BPE ya ce an yi wannan ne 2014 domin gina gidajen ma’aikata, amma a karshe ma’aikatan ba ta ba su samu damar cin moriyar tsarin ba.
Okoh ya ce a 2015 aka bada umarnin dauke duk wasu kudi a maida su asusun bai-daya na TSA a CBN, wannan ya sa aka fara shirin dawo wa BPE kudinta.