Kaicho Mutan Arewa: Mu Farka Lissafin mu Akwai Gyara

Daga zaid Ayuba Alhaji

Masu iya magana sunce “tun ran gini tun ran zane”.

Shuwagabannin mu na baya sun zana iya zanawar su, daga lokacin da aka farga da kyakkyawan shirin su akan Arewa,aka afka musu da sunan juyin Mulki.

ubangiji ya gafartawa su sardauna, Tafawa balewa da sauran Jaruman mu.

lissafin mutanen Arewa ya soma samun naqass, daga lokacin da mukai sake da koyarwar addinan mu, muka gurgunta al’adun mu, muka tarwatsa aqidun mu, muka bayyana dabarun mu, muka kekketa mutuncin mu,muka yarda da fallasa bambance-bambancen dake tsakanin mu, muka yarda darunguman wasun mu amaimakon kawunan mu.

daga wannan lokaci, muka soma afkawa cikin iftila’in zamani.

ALLAH ka gafartawa Mutanan Arewa.

lallai tuwo bai isa yaiwa tukunya cin fuskar baqi ba, koda ta haifeshi sai da tai masa gata.

Abin Mamakin shine kaga dan arewa na sukar arewa ba tare da wani tunani, kokari da tallafin yadda za’a gyara abinda zai iya gyaruwa ba, duk don ace ya waye ko kuma don aganshi daban daga cikin sauran faqirai da masu qarancin ilimi.

lallai ne mu gayawa dan arewa mai zagin Al’adun Arew; ya kuka da kansa.

wadan can ma da yake qoqarin burgewar, duk suna da nasu al’adun.

wasu ma giyace abin birgewar su, wasu kuwa tsirarar gangan, duk da yawan su al’adarsu barbarar wari kuma a haka suke alfahari da abinsu.

Ashe akwai dan’ dake fadin miyar mahaifiyarsa ba dadi? ko kuwa zamani ne ya koyawa dan’ giginya tunkude kallabin gyatumar sa?

daga kun fahimci ‘wadancen’ sun dau lardin kiran dayan ku ‘My brother’ to lallai abincika ya soma tafka aikin assha;

ko ya zaqe don son birgesu, ko cin mutunci ko yarfe ga al’adun Arewa, ko nuna kyama da qasqancin al’ummar arewa, ko kuwa bada qoyan  baya ga wani al’amari wanda baiyi daidai da arewa ba.

A yau Arewa ta rafke. Mun fantsama cikin dimuwa duk don sabida rashin hadin kai da kishin kai, mun narke acikin qunchi.mun bari sauran Yan Najeriya sun fimu baki;

Musamman ma kafafen yada labarai.  ayi mana qage iya son rai, a zage mu ta uwa ta uba, a ci zarafin mu dana iyayen mu kamar bayi, sannan yan boko aqidan cikin mu su jaddada goyan bayansu, ko kai tsaye ko a boye, musamman ma ta nuna halin ko in kula da irin cin mutunci.

Lallai “idan bera da sata toh daddawa ma da wari”!Mun bari shaye shaye yai mana katutu, kayan maye harda matan Aure, a mashayan;babu tsoho babu yaro, duk da a Arewa babu kamfanonin sarrafa qwaya, mun zura ido mun bar ya’yan hofi nata shigo mana da kayan maye duk da munsan yadda zamu daqile su. Yau Arewa ta zama kwata ko Mahauta,kullum sai dai a kwantarda jama’a a yanka, babu sauqi babu qyara, kullum muna ta ‘raragefe da gunaguni’ mun kasa tsaya kyam mu gayawa gwamnatocin mu gaskiya, ko don tsoro ko munafunci, ko soyayya ta siyasa ko kuma don abin bai shafemu ba kai tsaye.

Ya mu al’ummar Arewa!lallai yaqi nata cin mu,dan zamba abin lissafi, ana ta kashemu ta ko ina mu kuwa ‘muna ta cin kasuwar gafiyar baidu’.

An gwara kanmu da rabe-raben aqidun addini, an tarwatsa mu ta fuskar siyasa, an bata tattalin arzikin mu da rashin tsaro, an dakushe mu da rashin ilimi yadda ta kamata, an gurgunta mu da kayan maye, an dauke hankalin mu da rudiyar zamani da wayewa, ana ta kashe mu kamar kiyashi, an turmushe mu da kafafen yada labarai kamar awaki, an maidamu kamar bayin farko.

Mukuma, mun qi daukar kakkausan mataki, kullum sai dai muyi ta jimami amma a banza.

Dattijan Arewa Don ALLAH mu Farka, duk wani sarki ko limami, Attajirai da Mawallafa,Ma’aikata, Marubuta, Malaman Makarantu, qungiyoyin mata,shuwagabannin matasa daduk wanda yake da wata dama, don ALLAH mu farka.

An kusa kaiwa inda za’a mamaye mu da yaqin qare dangi,rankatakaf a maidamu inda bazamu iya farfadowa ba har abada.

Hassadar ta take cin mu a tsakanin mu, rainuwa da qyashin girmama masu kima, son kai da rashin hangen nisa, rashin bin diddigi da binciken qwaqwaf akan lamuran da suka kamata,duk suna cikin masifun da suke bibiyar mu.

dukkan mu muna da gudun mawar da zamu bada wajen kare iljamar Arewa,cigaban al’ummar mu,hadin kan matasa, dawo da kima da martabar al’adun mu na Arewa dangane da daraja manya,girman malaman addini, juriya da dagewa kan neman yancin kai,rungumar matsalar dayan mu kamar dukkan mu abin ya shafa, dauriya akan amfanin gobe sama da kwadayin yau, saudaukar da abin kai don cigaban al’umma da sauran dabi’un dasu sardauna suka ginu akansu.

don ALLAH don son Manzon ALLAH muyi qoqarin aiki wanna matashiya ga duk wani mai kishin Arewa, ko Matashi ko dattijo,yan’uwan mu talakawa ko attajirai, mu sani duk muna da gudun mawar da zamu bada, lokacin bai qure ba amma fa idan mukai da gaske, hadin kan mu da tattaunawa akan matsalolin mu,jan ido da daukan kakkausan mataki na rubuce-rubuce, zauren tuntuba da nuna rashin yadda akan matsalolin da suka  shafemu da kasuwanci, tarbiyya, tattalin arziki da duk wani abu daya shafi cigaban mutan Arewa da yankin Arewa gaba daya.Don haka nake kira da fitar da tsarin ‘DEVELOPMENTAL AGENDA OF NORTHERN NIGERIA [DANNAGENER]’.

Zaid Ayuba Alhaji,

[sir. kuli kuli].

Daya Daga cikin matasa Yan’gwagwarmaya Masu Tunanin Gobe.

08069835881 [email protected]

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here