Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da Sababbin Jiragen Yaƙi Guda 3 ga Rundunar Sojojin Sama

 

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da shigar da sabbin jiragen yaƙi uku zuwa cikin kayan aikin NAF.

Shugaban wanda ministan tsaro, Bashir Magashi, ya wakilta, yace wannan babbar nasara ce da gwamnatinsa ta samu na cika alƙawarin da ta ɗauka.

Shugaban rundunar NAF, Air Marshal Oladayo Amao, yace a ƙarƙashin wannan gwamnatin sun samu jiragen yaƙi 23 daga 2018 zuwa yanzu.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ranar Alhamis, ya ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi guda uku da gwamnatinsa ta siyo wa rundunar sojojin sama (NAF), kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Shugaban ya miƙa jiragen ne a sansanin sojin dake Makurɗi yayin bikin cikar NAF shekaru 57 da kafuwa.

Shugaba Buhari, wanda ministan tsaro, Bashir Magashi, ya wakilta yace jiragen yaƙin JF-17 da aka ƙara zuwa kayan aikin NAF zasu taimaka sosai wajen yaƙin da rundunar take yi da yan ta’adda, yan bindiga da sauran manyan laifuka da ƙasar ke fama dasu.

Shugaban ya kuma jinjina wa yan Najeriya bisa namijin kokarinsu na ƙin amincewa da wasu ɓata gari dake ƙoƙarin raba ƙasar nan.

Yace:

“Wannan bikin miƙa waɗannan kayan aikin yana da matuƙar muhimmanci a waje na, sabida wata alama ce dake nuna mun fara cika alƙawurran da gwamnatin mu tayi na ƙara yawan makamai da kayan aiki ga jami’an soji da sauran jami’an tsaro.”

“Ina kira ga yan Najeriya masu kokarin bin doka da su cigaba da zama tare da juna, kada su kalli banbancin ƙabila, yare ko addini domin hakan ne zaisa Najeriya ta cigaba da zama ƙasa ɗaya.”

A ɓangarensa, shugaban rundunar NAF, Air Marshal Oladayo Amao, ya bayyana cewa har yanzun ana tsammanin isowar ƙarin jiragen yaƙi 20 zuwa Najeriya daga watan Yuli na wannan shekarar.

Yace: “A ƙarkashin wannan gwamnatin mun samu sabbin jiragen yaƙi 23 zuwa cikin kayan aikin mu daga shekarar 2018 zuwa yanzun.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here