‘Yan Bindiga sun Kashe ‘Dan Sanda a Jahar Imo

 

Wasu ‘yan ta’adda sun hallaka jami’in dan sanda a wani yankin jahar Imo a kudancin Najeriya.

Rahoto ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun yi shiga cikin kakin soja sadda suka hallaka jami’in.

Ana ci gaba da hallaka jami’an tsaro a yankin kudu, lamarin da ya jawo tashin hankali a kasar.

A jiya ne rundunar ‘yan sanda reshen jahar Imo ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga cikin kakin soji sun kashe wani jami’inta, Sajan Loveday Obilonu, a hanyar Okwu Uratta da ke Owerri, jahar Imo, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Abutu Yaro, ya bayyana hakan ga manema labarai a Owerri, ta bakin jami’in hulda da jama’a na yan sanda na jahar, Bala Elkana.

Abutu ya ce Sajan Loveday na daga cikin jami’an da aka tura don kare ‘yan jahar daga masu aikata laifuka.

A bincikensu na farko, ya kara da cewa wasu ‘yan bindigan sun kashe jami’in ne bayan da suka gane shi dan sanda ne kuma yana dauke da bindiga.

Duk da haka, rundunar ‘yan sanda ta Imo ta ce ta fara gudanar da bincike don kamo wadanda suka aikata aika-aikar.

A yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudu, tsageru na ci gaba da kashe jami’an tsaro da kuma kone-konen ofisoshin jami’an tsaro.

A farkon shekerar nan, wasu ‘yan daba sun kai hari ofishin yan sanda na Umuoba da ke karamar hukumar Isiala Ngwa ta Arewa a jahar Abia a ranar Litinin, 1 ga watan Fabrairu inda suka kashe wani sifeton ‘yan sanda, Premium Times ta ruwaito.

Wani rahoton jaridar Punch, ya bayyana yadda aka yi asarar jami’an tsaro sama da 120 tare da kone-konen ofisoshin hukumonin tsaro na ‘yan sanda da gidan yari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here