Sauya Shekar Gwamna Ben Ayade Daga PDP Zuwa APC: Jam’iyyar PDP ta Shiga Taron Gaggawa

 

Kwamitin gudanarwan uwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shiga ganawar gaggawa a hedkwatar jam’iyyar dake Abuja sakamakon sauya shekar gwamnan jahar cross Ribas, Ben Ayade, daga PDP zuwa APC.

Leadership ta ruwaito cewa mambobin kwamitin sun taru a ofishin shugaban jam’iyyar gabanin ganawar gaggawan.

Har yanzu ana cikin ganawar kuma yunkurin ji ta bakin kakakin majalisar ya ci tura. Mun kawo muku cewa gwamnan jahar Cross Ribas, Ben ayade, ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Gwamna Ayade ya sanar da hakan ne da safiyar Alhamis a ganawar da yayi da gwamnonin APC shida da suka kai masa ziyara gidan gwamnatin jahar.

Ben Ayade, gwamnan jahar Cross Rivers ya bukaci sauran gwamnoni a tsohuwar jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party, PDP, su dawo jam’iyyar All Progresives Congress, APC.

“Akwai bukatar mu hada hannu da Shugaba Buhari a kokarinsa na inganta da habbaka lamuran kasar nan. Ina kira ga sauran gwamnoni su yi koyi da ni su fahimci dalili na na shiga APC,” Ayade ya ce.

“Ya kamata mu yi aiki tare da shugaban kasa domin cigaba da hadin kan Nigeria. Akwai bukatar dukkan mu mu zauna tare da Shugaban kasa a teburi daya mu ceci Nigeria.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here