Rashin Jituwa Tsakanin Iyalan Marigayi Janar Ibrahim Attahiru da Rundunar Sojojin Najeriya

 

An samu rashin jituwa tsakanin iyalin COAS Ibrahim Attahiru da rundunar sojojin Najeriya.

Iyalansa sun jaddada cewa ba za a birneshi a akwatin gawa ba amma rundunar tace sai an bi al’adar sojoji.

Da kyar aka shawo kan iyalansa sannan suka amince aka kara fadin kabarinsa yadda akwatin zai shiga.

An samu karamar hayaniya a ranar Asabar tsakanin iyalan marigayi shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da rundunar sojin Najeriya yayin birne shi.

Wannan rashin jituwan ne ya kawo jinkirin birne shi domin kuwa iyalansa sun jaddada cewa ba za a birne shi da akwatin gawa ba sai dai yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Amma wasu manyan hafsoshin sojoji sun jaddada cewa dole ne a birne gawar Attahiru kamar yadda al’adar sojoji ta tanadar, The Punch ta ruwaito.

Bayan wani lokaci, manyan sojojin sun shawo kan iyalansa kuma an fadada kabarinsa zuwa yadda zai dauka akwatin gawar.

Attahiru da sauran sojoji 10 sun yi hatsarin jirgin sama ne a ranar Juma’a a filin sauka da tashin jiragen sama dake Kaduna.

An gano cewa jirgin dauke da sojoji mai lambar rijista 5N-R203 zai sauka a sansanin dakarun sojin sama dake Mando Kaduna amma ya koma ya sauka a filin jirgin sama na Kaduna saboda yanayin gari mara kyau. Baya ga Attahiru, akwai Birgediya Janar Ahmed Kuliya, O Olayinka da MI Abdulkadir, Manjo N Hamza, Manjo LA Hayat, Sajan O Adesina da Umar. Akwai matukan jirgin OM Oyedepo, TO Asaniyi da AA Olufade.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here