Shugaba Buhari ya Cika Alƙawarin da ya ɗauka na Gudanar da Sahihin Zaɓe – Lai Mohammmed
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cika alƙawarin da ya yiwa ƴan Najeriya kan zaɓe.
Ministan Buhari, Lai Mohammed shine ya bayyana hakan inda yace ƴan Najeriya basu bin Buhari bashin gudanar da sahihin zaɓe.
Lai Mohammed yayi ƙarin haske kan dalilan da ya sanya zaɓen bana ya kasance sahihi.
Abuja- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya cika alƙawarin da ya ɗauka na gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan.
Ministan watsa labarai da al’adu, Lai Mohammed, shine ya bayyana hakan inda yace shugaban ƙasar zai bar tarihin yin ingantaccen zaɓe a shekarar 2023. Rahoton Vanguard.
Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wasu gidajen watss labarai na ƙasashen waje.
Read Also:
Yace domin cika alƙawarin da shugaban ƙasan yayi na dawo da martabar zaɓe a ƙasar nan, ya yanke shawarar ƙin fifita wata jam’iyya ciki har da jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress, APC, a lokacin zaɓen. Rahoton Punch.
Lai yace a lokacin zaɓen, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa babu wanda yayi amfani da jami’an tsaro domin yin maguɗi, inda aka tabbatar da cewa babu wani ko wata jam’iyya da ta samu fifiko.
A kalamansa:
“Hujjar cika wannan alƙwarin nasa shine jam’iyyar shugaban ƙasa ta faɗi zaɓen shugaban ƙasa a jihar sa ta Katsina.”
“Haka kuma, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya faɗi a jihar sa ta Legas, yayin da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya faɗi a jihar sa ta Nasarawa a hannun Labour Party.”
“Darekta janar na kamfen ɗin shugaban ƙasa na jam’iyyar mu shi ma ya sha kashi a hannun PDP a jihar Plateau.”
“Babu abinda ya ƙara tabbatar da sahihancin waɗannan zaɓukan face yadda ba ayi maguɗi ba a jihohin da manyan jiga-jigan mu suka fito ba.”
Ministan ya kuma ƙara da cewa jam’iyyar APC ta sha kashi a jihohi huɗu waɗanda ke da yawan mafiya ƙada ƙuri’u a zaɓen, Katsina, Kano, Kaduna da Legas duk kuwa da cewa jihohin suna ƙarƙashin ikon jam’iyyar ne.