Cire Tallafin Man Fetur zai Kara Jefa Talaka Cikin Matsi – Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya

 

Wata kungiyar matasan arewacin Najeriya ta ce ba zata amince da yunkurin cire tallafin man fetur ba.

Kungiyar ta ce cire tallafin zai kara jefa talaka cikin matsi akan wanda ya ke fama da shi na tsadar rayuwa.

Kungiyar ta yi kira ga sauran kungiyoyi da su tashi tsaye wajen neman ceto talaka daga abin da ake shirin yi.

Jihar Kaduna – Wata kungiya, kungiyar matasan arewacin Najeriya, ‘Northern Youth Council of Nigeria’, ta gargadi gwamnati tarayya game da yunkurin cire tallafin mai, tana mai cewa ba za a juri haka ba, The Punch ta rahoto.

Yayin nuna adawa da cire tallafin, kungiyar ta bayyana irin matsalar da hakan zai haifar ga yan Najeriya “da dama su ke cikin matsin tattalin arziki.”

Abin da yasa muke adawa da cire tallafin mai – Isa Abubakar, Shugaban Northern Youth Council of Nigeria.

Shugaban kungiyar, Alhaji Isa Abubakar, wanda ya bayyana haka a Kaduna ranar Alhamis, ya bayyana tsoron kada wasu tsiraru su yi awon gaba da duk wani tallafi da zai rage radadin cire tallafin, kamar yadda ya faru da tallafin COVID-19.

Haka nan, kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta sake duba batun cire tallafin, ta na cewa hakan zai kara kunci a rayuwar talaka, wanda bukatun yau da kullum ke gagara.

Ta kuma shawarci gwamnati da ta mayar da hankali wajen samar da aikin yi don bunkasa tattalin arziki.

“Ba za mu iya jure sake jefa mutanen Najeriya a wahala ba, musamman matasa da ke fama da tsananin rashin aikin yi da rashin ba su dama,” in ji shi.

Ya ce akwai hukunci ga duk wanda ke son jefa yan Najeriya wani hali musamman idan bukata ta dawo da shi lokacin siyasa.

“Su tuna yadda aka kayar da wasu gwamnoni a zaben da ya gabata za su fahimci cewa yanzu iko na hannun talakan Najeriya.

Yan Najeriya ba za su manta ba. “Kungiyar matasan ta ce ba za ta amince da duk wani yunkuri na cire tallafin mai ba kuma ta na kira ga sauran kungiyoyi da su tashi su taya yan Najeriya yaki,” a cewar shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here