Shugaba Muhammadu Buhari ya Shiga Ganawa da Shugaban Hukumar INEC
Shugaba Buhari ya gana da shugaban hukumar INEC biyo bayan hare-hare da ake kai wa ofisoshin hukumar.
A tare da shugaban na INEC akwai kwamishinoni biyar da aka yi tattaunawar dasu a Abuja.
Ana sa ran sun tattauana mafita ne kan karuwar hare-hare da ake kai wa ofishoshin INEC a fadin kasar.
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gana da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, Channels Tv ta ruwaito.
Read Also:
Farfesa Yakubu ya kasance tare da kwamishinonin INEC guda biyar a taron, wanda aka yi a dakin taro na Uwargidan Shugaban Kasa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Taron na iya zama mai nasaba da hare-haren da aka kai kan cibiyoyin INEC na baya-bayan nan a duk fadin kasar.
Rahoton Premium Times ya ruwaito shugabn na INEC a ranar 27 ga Mayu, yana cewa an kai wa ofisoshi da wuraren aikinta hari sau 41 a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Sai dai, a cikin makonni hudun da suka gabata, ofisoshin hukumar guda 11 ko dai an cinna musu wuta ko an lalata su, a cewar shugaban na INEC.
A ranar Litinin, hukumar zaben ta sha alwashin gudanar da zaben gwamnan Anambra, wanda aka shirya za a yi a ranar 6 ga Nuwamba, duk da karuwar matakan rashin tsaro a fadin kasar.