NANS ta yi Kira ga Hukumar Shirya JAMB da ta Sake ƙara Sati Biyu Domin Baiwa Wasu ɗalibai Daman Yin Rijista

 

Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) reshen Kaduna ta nuna rashin jin daɗin ta kan matakin wajabta amfani da profile code wajen yin rijista.

Shugaban NANS na Kaduna, Huzaifa Bello, yace dubbannin ɗalibai ne zasu rasa damar yin jarabawar saboda rashin mallakar lambobin.

Yayi kira ga hukumar da ta sake duba yuwuwar ƙara wa’adin rijista ga ɗaliban da basu samu damar yi ba saboda wannan matsalar.

Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) reshen jahar Kaduna ta nuna damuwarta ganin cewa dubbannin ɗalibai ka iya rasa damar zama jarabawar JAMB ta wannan shekarar saboda matsalolin da suke fuskanta da NIN/profile code, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Shugaban NANS na jihar Kaduna, Huzaifa Bello, a wani jawabi da ya fitar, ya nuna rashin amincewarsa da matakin da hukumar JAMB ta ɗauka.

Saboda haka shugaban yayi kira ga hukumar da ta ƙara wa ɗaliban dake son yin rijista lokaci kafin ta rufe damar rijistar jarabawar ta bana.

Maimakon Matakin da hukumar ta ɗauka na cewa duk ɗalibin da ya samu matsalar yaje hedkwatar JAMB ta jaharsa su masa rijista.

Mr. Bello yace: “JAMB ta jawo dubbanni ɗalibai ba su yi rijista ba saboda sun kasa samun profile code kafin wa’adin 27 ga watan Mayu da hukumar ta saka ya cika.”

“Mun samu kiraye-kiraye daga ɗalibai da iyayen yara waɗanda suka nuna rashin jin daɗin su akan matakin da JAMB ta ɗauka na wajabta amfani da profile code kafin yin rijista.”

“Daga ƙididdigar da muka samu, hukumar tayi rijistar dalibai 1.3 miliyan ne kacal yayin da a shekarar data gabata ta samu dalibai miliyan biyu.”

Bello yayi kira ga hukumar shirya jarabawar JAMB da ta sake ƙara sati biyu domin baiwa wasu ɗalibai daman yin rijista.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here