Ba Shugaba Buhari ne ya Gaza ba, Sai Dai ba a Bashi Shawara Mai Kyau – Solomon Dalung

 

Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung ya koka kan yadda wasu suka kange shugaba Buhari da masu bashi shawara.

Dalung ya kuma bayyana ra’ayinsa kan cewa, ba shugaba Buhari ne ya gaza ba, sai dai ba a bashi shawara mai kyau .

Ya kuma yi kira ga a taya shugaban da addu’ar Allah ya kiyaye shi daga wannan mummunan abu da ya zagayeshi

Abuja – Tsohon ministan wasanni da harkokin matasa, barista Solomon Dalung, ya koka kan yadda wasu makusanta shugaban kasa Muhammadu Buhari a mulki suke kange shi da masu kokarin ganin sun daura shi a turba ta gari da yi wa ‘yan kasa hidima.

Dalung ya kuma bayyana cewa, na kusa da shugaban sukan ba da uzurin bogi na cewa, akwai annobar Korona don haka ba za a iya gana wa da shugaban ba.

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da wakilinmu a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021.

Yayin da aka tambayeshi game da aikin da na kusa da shugaban ke yi wajen ganin sun wanke Najeriya daga kunya a idon duniya, musamman ta fannin tsaro, Dalung ya bayyana cewa:

“Yana yiwuwa wadanda suke kange shugaban kasa yanzu basa son a bashi wani shawara kan abin da yake faruwa. Kenan, suna niyyar su bashi kunya da rushe kyakkyawar manufa da yake dashi shiyasa suka hana da kange mutane zuwa jikinsa.

“Ai yana zuwa taro, ai yana karbar baki, muna ganin yana karbar mutane, wadannan mutanen basu da corona ne? ko sai mu da zamu zo mu ganshi ne zamu cutar dashi? ”

Ana zargin shugaba Buhari ya gaza wajen magance matsalar tsaro, shin haka ne?

A bangare guda, Dalung ya kuma bayyana yadda mutane da dama ke ganin shugaba Buhari ya gaza wajen inganta tsaro a Najeriya, amma a nasa bangare, ya ce shugaban bai gaza ba sam-sam.

“Ina ganin kamar matsalar tsaro da aka shiga ciki, wanda ‘yan Najeriya suke fama dashi kowacce rana, kuma ana zargin shugaban kasa cewa ya gaza.

Ina ganin ba wai lallai ya gaza bane, amma wane irin bayani yake zuwa gareshi?

“Shin abubuwan da suke faruwa yana jin su kamar yadda suke faruwa?

“Amma a nawa tunanin shugaban kasa ya shiga hali na mutane wadanda za su bashi shawara mai kyau sai dai su je kusa dashi su kadai. Wannan a yi addu’a ga Allah, Allah ya taimaki shugaban kasa ya fita cikin wannan hali.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here