Shugaba Buhari ya Mika Godiya ga Wadanda Suka Aika Masa da Katunan Taya Murnar Cika Shekara 80 a Duniya

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya mika godiya ga wadanda suka aika masa da katunan taya murnar cika shekara 80 da haihuwa a duniya.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya aikewa manema labarai, ya ce cikin barkwanci shugaba Buharin ya ce ma’aikata ba su samu damar shagali a ranar ba: ”saboda da gangan na sanya ranar dawowata daga Amurka, kwana daya bayan wannan rana, domin kaucewa duk wasu bukukuwa da za a yi.”

Sanarwar ta ce, da ya ke yin jawabi a shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnatin tarayya Mista Boss Mustapha, da manyan bakin da suka je gida domin taya shi murna, shugaba Buhari ya ce rana irin wannan daya ta ke da kowacce rana a bakin aiki.

Shugaba Buhari ya karanta sakon da ke cikin wani katin taya murna da manyan jami’an fadar suka bashi, a bainar jama’a, ya na cewa; ”a madadin daukacin ma’aikatan da ni kaina, mu na taya ka murnar zagayowar ranar Haihuwar jajirtacce shugaba, uban kasa, kuma babanmu.

Shugabanmu ne ya zama gwarzo a taron koli tsakanin kasashen Afirka da Amirka da aka gama kwanakin nan, mu na alfahari da kai, muna murnar ka dawo bakin aiki lafiya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here