INEC da NBC da Masu Ruwa da Tsaki Sun yi Taro a Kan Lamarin Zaben 2023

 

Hukumar zabe ta Najeriya INEC, da hukumar da ke sa ido kan kafofin watsa labarai ta NBC da sauran masu ruwa da tsaki a kan lamarin zabe sun gudanar da wani taro a Abuja, babban birnin kasar.

Shi dai wannan taron an yi shi ne da zummar jawo hankalin jam’iyyun siyasa da kafofin watsa labarai don ka da su bari a yi amfani da su wajen halasta kudin haram a lokacin zaben 2023.

Taron na masu ruwa da tsaki kan maganar kawar da yin amfani da kudi a zabe mai zuwa ya kunshi bangarori daban-daban.

Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahamud Yakubu, ya ce sun cimma daidaito a tsakanin dukkan mahalarta taron.

Wasu dai daga bangaren mahalarta taron sun yi korafi kan maganar kayyade fitar da kudi daga asusun banki duk rana da babban bakin Najeriya ya sanar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here