Shugaba Buhari da Hafsoshin Tsaro Sun Shiga Ganawar Gaggawa a Abuja
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawar gaggawa da hafsoshin tsaro a babbar birnin tarayya Abuja.
Taron na gudana ne a safiyar yau Litinin, 31 ga watan Oktoba, yayin da ake tsaka da fargaba kan yuwuwar kai hare-hare a birnin kasar.
Ofishin jakadancin Amurka ta yi gargadi kan yuwuwar kai hare-hare a wasu yankunan babban birnin tarayyar kasar.
Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wani taron gaggawa da manyan hafsoshin tsaro na kasa a kan lamarin tsaro.
Kamar yadda mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwar zamani, Buhari Sallau ya sanar a shafinsa na Facebook, taron na gudana ne a safiyar yau Litinin, 31 ga watan Oktoba, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Read Also:
Ana sanya ran za su sake bita da kuma karfafa lamarin tsaro a kasar nan.
Idan za ku tuna, ofishin jakadancin Amurka ta yi gargadi kan yiwuwar kai hare-hare a wasu yankunan babban birnin tarayya Abuja.
Hakan ya haifar da tsoro da fargaba sosai a tsakanin al’umma domin kasashen US da UK sun shawarci yan kasarsu da su bar Abuja.
Sai dai kuma, da take martani kan lamarin, hukumar DSS ta bukaci yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu amma dai su zamo masu lura.
A wata sanarwa daga kakakinta, Dr. Peter Afunanya, DSS ta shawarci yan Najeriya da su yi taka-tsantsan, sai dai ta bayar da tabbacin cewa za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya.
Ta bukaci yan Najeriya da su sanar da hukumar bayanai da ke da nasaba da barazana ko ayyukan da basu yarda da shi ba.