Na Siyar da Gidajen Mai Guda Biyu Domin Daukar Nauyin Harkokin Rusasshiyar Jam’iyyar NADECO – Tinubu

 

Bola Tinubu ya bayyana cewa yana daukar nauyin harkokin siyasarsa ne da kudin da ya samu bayan ya siyar da gidajen mansa guda biyu.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya yi bayanin cewa yana da gidajen mai guda biyu a Landan wanda matarsa ce ke kula da su.

A cewar Tinubu, kudaden da ya samu daga siyar da kadarorin nasa sune ya yi amfani da su wajen daukar nauyin rusasshiyar jam’iyyar National Democratic Coalition (NADECO).

Abuja – Bayan yan Najeriya da dama a fadin duniya sun nemi jin ta bakinsa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya magantu kan tushen arzikinsa.

Yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin kungiyar NAPOC a Abuja, Tinubu ya bayyana cewa yana da gidajen gas biyu a birnin Landan, jaridar The Nation ta rahoto.

A cewar tsohon gwamnan na jihar Lagas, matarsa Remi ita ce ke kula da gidajen man wanda daga bisani ya siyar da su domin daukar nauyin rusasshiyar jam’iyyar National Democratic Coalition (NADECO).

Ya ce:

“Ina da gidajen mai biyu a Landan, wanda matata ke kula da su. Na siyar da gidajen man biyu domin daukar nauyin harkokin rusasshiyar jam’iyyar National Democratic Coalition (NADECO).”

Bayanin Tinubu kan tushen arzikinsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa watakila tsohon gwamnan ya yi wasu badakaloli kafin a sanshi a matsayin dan siyasa.

Da yake ci gaba da jawabi, Tinubu ya kuma bayyana cewa shi ya dauki nauyin NADECO tare da Alfred Rewane duk da cewar ya dade da mayar da hankali wajen zuba jari a kasuwanci daban-daban kafin ya shiga harkar siyasa.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here